Kungiyar Ci Gaban Shakwata tare da Huffazul Qur’an sun karrama Shugaban Ƙaramar Hukumar Chanchaga

Daga Awwal Umar, Kontagora

Kungiyar Ci Gaban Shakwata (Shakwata Development Association and Cooperatives) ta Jihar Neja, tare da haɗin gwiwar Kungiyar Huffazul Qur’an and Scholars Association of Nigeria, sun karrama Shugaban Ƙaramar Hukumar Chanchaga, Hon. Dr. Mustapha Jibrin Alheri, bisa gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban al’umma.

Da yake jawabi tun farko, Babban Limamin Masallacin Juma’a na Shakwata kuma Shugaban Kungiyar Huffazul Qur’an and Scholars Association of Nigeria, Gwani Amb. Hussaini Abubakar Shakwata, ya bayyana cewa an shirya wannan karramawa ne sakamakon nasarar da Dr. Mustapha Jibrin Alheri ya samu a zaɓen ƙananan hukumomi da ya gabata, tare da irin ayyukan alheri da ya aiwatar a garin Shakwata.

Gwani Hussaini Abubakar Shakwata ya ce ba za a taɓa mantawa da gudunmawar da Dr. Alheri ya bayar a garin Shakwata ba, domin kusan dukkan manyan ayyukan ci gaba da ake gani a garin suna da alaƙa da shi. Ya ce shi ne ya gina Masallacin Juma’a da ake gudanar da sallah a ciki, sannan ya samar da wutar lantarki ta solar a masallacin da wasu sassan gari. Ya ƙara da cewa Dr. Alheri ɗan asalin garin ne mai kishin addini da al’umma.
Ya kuma bayyana cewa almajiran tsangaya sun amfana ƙwarai da gaske daga gudunmawar Dr. Alheri, musamman wajen tallafa musu da koyar da sana’o’in hannu, abin da ya taimaka wajen dogaro da kai ga almajirai da dama. Wannan ne ya sa, in ji shi, suka ga dacewar shiga sahun masu karrama shi domin ƙara masa ƙwarin gwiwa.

A nasa jawabin, Shugaban Matasan Shakwata, Malam Abdullahi Danladi Kpasi, ya ce tabbas al’ummar Shakwata ba za su taɓa mantawa da irin gudunmawar wannan bawan Allah mai kishin garin haihuwarsa ba. Ya ce ayyukan alherin da ya yi sun isa su sa al’umma su ci gaba da mara masa baya.

Sai dai ya yi kira ga Dr. Mustapha Jibrin Alheri da ya duba yiwuwar gyara da bunƙasa asibitin garin, kasancewar Shakwata na ci gaba da faɗaɗa da ƙaruwa. Ya ce ana fatan za a ɗaga matsayin asibitin zuwa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Farko (PHC) domin sauƙaƙa samun kulawa ta gaggawa ga al’umma.

A nasa bangaren, Hon. Abubakar Gwamna, tsohon Shugaban Ƙaramar Hukumar Bosso kuma ɗan Majalisar Dokokin Jihar Neja mai wakiltar Bosso, ya shawarci Dr. Alheri da ya ƙara jajircewa wajen hidimar jama’a. Ya ce Ƙaramar Hukumar Chanchaga na daga cikin manyan ƙananan hukumomin da Jihar Neja ke buƙatar a ba su kulawa ta musamman, kasancewarta a fadar gwamnatin jiha.

Ya bayyana Dr. Alheri a matsayin matashi mai kishin aiki da jajircewa, yana mai cewa yana da gogewa sosai, musamman duba da cewa ya taɓa riƙe muƙamin Kwamishinan Lafiya na jihar, inda kowa ya shaida irin gudunmawar da ya bayar a fannin kiwon lafiya.

Da yake jawabin godiya, Shugaban Ƙaramar Hukumar Chanchaga, Hon. Dr. Mustapha Jibrin Alheri, ya yabawa matasan Shakwata da Kungiyar Huffazul Qur’an bisa shirya wannan gagarumin biki na karrama shi. Ya sha alwashin ci gaba da jajircewa wajen amfani da duk wata dama da Allah ya ba shi domin tallafa wa harkokin addini da kuma bunƙasa ci gaban garin haihuwarsa.

A nasa jawabin, Alhaji Umar Damidami, Dagacin Shakwata, ya bayyana tarihin Dr. Mustapha Jibrin Alheri, inda ya ce ɗan asalin garin Shakwata ne, kuma kakanninsa sun bayar da gagarumar gudunmawa wajen ci gaban Masarautar Minna.

Bayan kammala taron, Dagacin Shakwata ya jagoranci tawagar baki da mutanen gari zuwa ziyarar kaburburan iyayen Dr. Mustapha Jibrin Alheri, domin tunawa da tarihi da kuma yi musu addu’a.

An gudanar da taron ne a filin makarantar firamare da ke cikin garin Shakwata, a ranar Asabar da ta gabata.

Post a Comment

0 Comments