Sabon Shugaban AFAN Ya Nemi Rangwamen Kayan Noma Don Ceto Manoman Nijeriya


Kungiyar manoma ta Nijeriya, AFAN, ta bukaci gwamnatoci su taimaka wa manoma da kayan aiki na zamani, kamar famfon ban ruwa na solar domin gudanar da noman rani yadda ya dace. 

Kungiyar ta koka kan asarar da manoman Æ™asar ke cewa sun tafka a noman daminar da ta wuce, saboda faÉ—uwar darajar amfanin gona da tsadar takin zamani da magungunan feshi.  

Ta kuma ce manoman Nijeriya ba su da damuwa idan sun sayar da amfanin gona cikin farashi mai sauki, to, amma su ma ya kamata a samar musu da kayan shuka masu rangwame. 

Honorabul Mohammed Magaji Gettaɗo shi ne sabon shugaban ƙungiyar ta AFAN ta ƙasa, ya kuma zanta da BBC Hausa a kwanan baya. Ya kuma fara ne da irin asarar da manoman Nijeriya suka tafka.

HONORABUL MAGAJI GETTAÆŠO: Kamar yadda muka faÉ—i, tabbas an samu wannan matsalar. Kuma in ka duba tun ina Sakataren yaÉ—a labarai nake magana a kai. Bara na hangi wannan, kuma na yi magana a kai. Amma duk da haka mu burinmu abincin ya yi sauÆ™i. Abin da muke so idan manomi ya samu taki a Naira dubu goma ko sha biyu, in ya yi tsanani dubu sha biyar, ya zo ya sayar da masararsa a farashi mai kyau, ba shi da damuwa ko kaÉ—an. Shi wanda bai yi noma ba zai ci abinci, shi kuma manomi ya ci riba, musamman idan gwamnatocin jihohi da na Tarayya suka taimaka farashin taki ga manoma ya sauko zuwa Naira dubu goma, wato takin Urea. In ya zo ya sayar da masararsa Naira dubu 15 ko 20 ba shi da asara. In ya sai da buhun masararsa, ka ga zai sai na taki buhu biyu. In an yi haka, an taimaki manomi, an taimaki al’umma, domin noman nan shi ne yake bai wa ’yan Nijeriya kashi 75% aiki, saboda haka in an yi musu wannan, an yi komai.

TAMBAYA: To, ta yaya za a yi wannan?

HONORABUL MAGAJI GETTAÆŠO: Aiwatar da hakan shi ne kamar yadda muka sha faÉ—i. A can baya an yi wannan. Da farko an bai wa manoma kayan aiki masu amfani bisa farashi mai kyau. Da an yi girbi, za ka ba da LBA, za su sai kayan manomi da sauri tun bai fita hannunsu ba. Mu ba ma goyon bayan a sayi abinci a hannun manoma bayan wata huÉ—u ko biyar, domin ya riga ya fita daga hannun manomi, wanda ya sha wahala ya noma. Muna so a saye shi tun yana gama girbi, lokacin tsananin sa bai wuce kashi 13% ba, kamar yadda suke so. A sai abinci a sa a sito a aje. Duk lokacin da aka buÆ™ata sai a sai da wa jama’a a kan farashin da ya dace. Ka ga ka taimake shi a amfanin gona, ka taimake shi ka saya a hannunsa.

Sannan a yi musu hanyoyin da za su fitar da amfanin gonarsu ba tare da wata matsala ba. Duk wata wahala da manomi yake yi, ya fitar da amfanin gonarsa, muna so a kau da matsalolin duka. Hatta haraji da mamomi yake biya kan amfanin gonarsa, yana cikin abin da muke Æ™oÆ™arin ganin an cire. In ka kai amfanin gonarkar, kamar masararka ko shinkafarka ko dabbarka, in ka kai kasuwa, to kar ka biya haraji. Wanda ya saya zai tafi da shi, shi ya kamata ya biya haraji. Irin wannan tsarin muke so a yi. Kuma za a yi shi. Domin abubuwa da yawa da Æ™ungiyar manoma ta Nijeriya ta yi a baya. Kuma ba na mantawa a Æ™arÆ™ashin gwamnatin Obasanjo, mai girma Admiral Murtala Nyako da duk gwamnonin Arewa an yi zama da su. Abin da muke nufi gwamnati ta É—auki mutane ta ba su kayan noma bashi mai yawa, ba wai É—an kaÉ—an ba. Iya abin da zai ishe ka na taki, iya abin da zai ishe ka na iri, a b aka. A yi lissafin kuÉ—insa. A bar ka ka yi amfani da shi a gonarka. Kana yin girbi, a zo a karÉ“i amfanin gonarka. In an karba, maimakon ana sai da buhun masara Naira dubu goma sha biyar a kasuwa, ita gwamnati ta karbe shi a kan Naira dubu 25. Ka ga ka samu Æ™ari, gwamnati kuma ba ta da faÉ—uwa. In an yi wannan shekara É—aya biyu, ina tabbatar maka, Allah kaÉ—ai ya san iya manoman da za su amfana. 

Sannan manomanmu mun gwada wannan a baya. Lokacin ina Sakataren Æ™ungiyar manoma a jihata ta Gombe, na nema wa al’ummarmu bashi, sun shaida, sun sani daga bankin manoma. Aka ba manoma bashi Naira dubu 150 zuwa Naira dubu 200, kuma aka yi inshora. Duk wanda ya samu matsala kamar ta yawan ruwa ko fari, muka bi duk aka biya musu ta bankin da suka karÉ“i bashin.

TAMBAYA: Duk shekara gwamnatocin jihohi kan yi bikin ƙaddamar da sayar da takin zamani. Shin kuna ganin hakan na tafiya yadda ya kamata?

HONORABUL MAGAJI GETTAƊO: Yawancin jihohin da suka yi, bara gwamnatin Tarayya ta bayar da taki kyauta. Gwamnoni ma suna yin iya nasu ƙoƙarin. Akwai gwamnan da ya bayar da taki a kan N1700. Amma kullum mu abin da muke cewa shi ne a riƙa ba da takin nan a kan lokaci. Muna so mu roƙi Gwamnoni su yarda su ƙaddamar da takin ne a lokaci ɗaya, kamar su ɗauki sati guda suna yi. Misali a ƙaddamar da shi daga 1 ga watan biyar zuwa 15 ga watan biyar. Duk jihohi su yi hakan, to a wannan lokacin sai farashin takin ya sauka. Har damina ta ƙare takin ba zai hau ba. Dalili shi ne idan ka zo ka ƙaddamar da naka, misali na jihar Gombe an ƙaddamar a watan biyar, wani Gwamnan bai ƙaddamar ba, sai a watan bakwai, to na Gomben nan, shi ne ɗan kwangilan da ka ba kwangilar ya kawo wa jiharka takin, zai zo ya saya a Gombe a wajen manoma, ya tafi da shi ya kai jihar da aka ba shi kwangila. Amma in lokaci guda za a ƙaddamar, to ka ga kowa zai tanadi takinsa. Wannan yana cikin abin da muke so za mu yi da gwamnoni. Su ƙara yawan abin da suke ba mutane, su ƙaddamar da shi a lokaci guda, su kawo taraktoci, hatta garmar shanu da shanun, a bai wa manoma, su yi noma su sayar da amfanin gona su biya.

TAMBAYA: WaÉ—anne Æ™udurori kake so ka gabatar a wannan wa’adin shugabancin naka?

HONORABUL MAGAJI GETTAÆŠO: Ba ma so kowane irin mutum ya yi fom, a ce manomi ya kawo kuÉ—i, saboda za a yi masa wani abu. Akan yi haka a ce ga fom, ka cike, ka sa hannu ka ba da dubu É—aya ko biyu ko uku, wani ma É—ari biyar. To, lokacin da mutane da yawa suka yanki fom É—in, ka ga shi wannan ya yi nomansa ya gama. A can baya, haka kawai sai ka ga mutum ya yi fom, ya ce wai na tallafin noman shinkafa da sauransu, alhali ma ba shi a cikin shugabannin masu noman shinkafa ko masara da sauransu. To, muna so mu tabbatar cewa manoma an daina karÉ“ar kuÉ—i daga wurin su. Mu kuma wayar da kansu cewa, kada wani manomi ya yarda wani ya zo ya ce masa ya ba da kuÉ—i za a tallafa masa. Duk manoman da suke cikin Æ™ungiyar AFAN, za mu yi musu rijista, mu yi ‘mapping’ gonakinsu, ta yadda bayanansu yana cikin kwamfuta, za a samu saukin ba su taimakon da suke buÆ™ata. Kuma muna so mu haÉ—a membobinmu da kamfanonin da suke ba da taimakon noma da taimakon sayen amfanin gona, kamar kamfanin Flour Mills, domin su taimaka al’ummarmu su samu sauki daga halin da suke ciki. Na sha faÉ—a ba manomin da ke buÆ™atar taimako dare da rana kamar Æ™aramin manomi, domin shi da cinsa da shansa duk a kan noman ne. Wani zai iya cewa shi ba zai yi noma ba, saboda ya yi tsada. Amma shi Æ™aramin manomi dole sai ya yi noman, saboda buÆ™atunsa sun ta’allaÆ™a kan noman.

TAMBAYA: Da yake ka ce manoma na buƙatar taimako, to ya ake ciki dangane da shirin gwamnatin Tarayya na ba manoma taimako?

HONORABUL MAGAJI GETTAÆŠO: Ina ganin wannan tambayar ta mutanen Ministry ce da banki. Amma mu abin da muke yi shi ne, muna so duk tsarin da za a fito da shi, to a tabbatar manoman ne suka amfana, ba manema ba. Asalin su manoman su amfana da bashin da za a bayar, a tabbatar an haÉ—a su da bankin manoma, kuma a yi musu inshora. Hakan zai rage asara. Babban abin da muke so duk manoma a yi musu rajista. In an yi haka, za a saukaka abubuwa da yawa.

Kuma gwamnatin Tarayya sun yi ‘programs’ shekaru biyu a jere na taimakon noman alkama da shinkafa da noman rani da sauran su. Kwanan nan mai girma Ministan noma ya je ya Æ™addamar da noman alkama bana a Maiduguri. To, fatanmu duk abin da suka É—auko, mu haÉ—u da su, a tabbatar manoman da suke buÆ™atar taimakon ne suka samu, daga sama har Æ™asa.

TAMBAYA: To, wane shiri kuke yi a ƙungiyarku ta AFAN na tunkarar noman rani na bana?

HONORABUL MAGAJI GETTAÆŠO: Kullum muna gaya wa mutane a shiga harkar noman ranin nan, domin shi yake ba da abinci fiye da yadda ake tsammani. Amma muna bi muna nema musu taimako na famfon solar, domin amfani da man fetur da dizal, duk ba zai yiwu ba a yanzu, saboda ya fi Æ™arfin farashin amfanin gona. Saboda haka muna bin gwamnatin Tarayya su sayi famfunan solar masu yawa, haka ma gwamnatocin jihohi su saya, domin akwai jihohin da ake noman ranin nan sosai. In suka samu suka ba manomansu kayan noman ranin nan da kake gani, to wannan zai taimaka mutane su yi abin da ya kamata, domin abin sha’awa, ina mai tabbatar maka, da na je wata gonar noman rani a jihar Gombe, za ka ga mashin na matasa sun fi hamsin, suna aje a jeji. Ina mai mashin É—in nan? Sun zo mutum uku a É—aya, sun shiga daji noman rani. Har da noma abin da ake kira gurom, wanda matan ‘yan’uwanmu Fulani suke goge baki da shi. An yi noman dankali da sauransu. Abin da kawai suke nema, taimakon gwamnatocin jihohi da na Kananan Hukumomi don bunÆ™asa noman su.

Post a Comment

0 Comments