Babu Abin da Ya Fi Alƙur’ani Gina Tarbiyyar Yara — Sheikh Kamilu

Daga Awwal Umar Kontagora

An bayyana cewa babu wata hanya da za a gina tarbiyyar yara a samu ingantaccen tsiro mai amfani gare su kamar karantar da su Alƙur’ani Mai Tsarki. Sheikh Muhammad Kamilu Minna ne ya bayyana hakan a yayin bikin walimar saukar Alƙur’ani tare da Mauludin Sheikh Ibrahim Nyass, wanda aka gudanar a garin Jita, da ke Ƙaramar Hukumar Bosso, a ranar Juma’ar makon nan.

Shehin malamin ya ce garin Jita an assasa shi ne bisa ginshiƙin tarbiyyar addinin Musulunci, yana mai bayyana cewa wanda ya kafa garin, Sheikh Usmanu Jita, yana daga cikin almajiran Sheikh Ibrahim Nyass, wanda ya ba shi sahalewa da izinin kafa cibiyar karantarwa a yankin Minna.

A cewarsa, tarihi ba zai taɓa mantawa da irin gudunmawar da magabata suka bayar ba wajen karantarwa da yaɗa addinin Musulunci a yankin.
A nasa jawabin, Babban Limamin garin Jita, Sheikh Abdullahi Usman, ya bayyana cewa ba su kauce daga tafarkin da magabata suka shimfiɗa na karantarwa ba. Ya ce a yau, idan ana maganar garuruwan da suka taka muhimmiyar rawa wajen yaɗa addinin Musulunci a Minna da kewaye, wajibi ne a ambaci Madako, Jita da Lapai, kasancewar dukkansu na daga cikin garuruwan almajiran Sheikh Ibrahim Nyass.

“Ina kira ga iyaye, kamar yadda suka haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen gina masallacin Juma’ar Jita, su ƙara haɗa kai wajen ƙarfafa harkar karantarwa, domin ilimi ya ci gaba da ginuwa a rayuwar yara masu tasowa,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa makarantar na buƙatar tallafi sosai domin ɗaukar nauyin malamai da ƙarfafa musu gwiwa wajen ci gaba da koyarwa. Ya kuma buƙaci iyaye da su tabbatar ’ya’yansu na ci gaba da neman ilimin addinin Musulunci. Ya bayyana cewa yara bakwai ne suka yi saukar Alƙur’ani a wannan karo — maza biyar da mata biyu, kuma dukkaninsu na tsakanin shekaru 12 zuwa 18.

A nasa bangaren, Dikko Muhammad Nasiruddeen Jita, Sarkin Fulanin Jita, ya ce kafuwar garin na kusan kaiwa shekaru 80 zuwa 90, inda ya bayyana cewa yawancin al’ummar garin an haife su ne a nan kuma sun tashi suna ganin irin gwagwarmayar da iyayensu suka yi wajen neman ilimin addini da yaɗa shi.

Ya ce tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya, babu wani gwamna da bai taɓa zuwa garin Jita neman goyon baya a lokacin zaɓe ba, sai dai Gwamna Umaru Mohammed Bago, amma duk da goyon bayan da al’ummar garin ke bai wa gwamnati, ba su taɓa samun tallafi ko gina wani muhimmin abin more rayuwa daga gwamnati ba.
“Ba mu da hanya, ba makarantar boko, balle asibiti. Duk abin da ka gani a nan ƙoƙarin matasanmu ne, duk da yawan jama’ar da muke da su,” in ji shi.
Dikko Nasiruddeen ya kuma ja hankalin al’ummar Fulanin Jita da su tabbatar kowa ya mallaki katin zaɓe, tare da mara wa gwamnatin Umaru Bago baya a zaɓe mai zuwa, domin ƙarfafa ƙoƙarinta na inganta rayuwar makiyaya, musamman ta hanyar kafa Ma’aikatar Kula da Jin Daɗin Makiyaya da Manoma a Jihar Neja.

A nasa jawabin, Malam Jamilu Isah, wani matashi a garin, ya yaba da tarbiyyar da iyaye suka bai wa matasan Jita, inda ya ce suna haɗa ilimin addini da na zamani. Ya ce a Jita ba su da matashi ko guda ɗaya da ke shan taba sigari, balle a same shi cikin aikata munanan ɗabi’u.

Ya yi addu’ar Allah Ya kare matasan garin daga munanan halaye da wasu matasa ke tsintar kansu a ciki a yau, tare da ƙarfafa musu gwiwa da su ci gaba da haɗin kai, jajircewa wajen neman na kai ta halastacciyar hanya.

Dangane da Mauludi kuwa, Malam Jamilu ya ce sun ɗauke shi a matsayin wata hanya ta ƙarfafa zumunci, inda ya ce taron ya haɗa ’yan uwa daga wurare daban-daban da kuma abokan zama, abin da ke nuna kyakkyawar fahimta da zaman lafiya a tsakaninsu.

An kwana ana karatun Diwani a daren Alhamis, yayin da bayan kammala sallar Juma’a aka gudanar da walimar tare da Mauludi a harabar Masallacin Juma’a na garin Jita.

Post a Comment

0 Comments