Daga Sani Muhammad Sani, Niger
Manyan shugabannin jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) sun kai ziyarar girmamawa ga tsohon Shugaban Mulkin Soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), da kuma tsohon Shugaban Ƙasa, Janar Abdulsalami Abubakar, a Minna, Jihar Niger, domin sake jaddada kudirinsu na tabbatar da dorewar dimokuraɗiyya a Nijeriya.
Tawagar SDP, ƙarƙashin jagorancin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2023, Yarima Adewale Adebayo, ta ziyarci dattawan ƙasar ne domin neman shawarwari da kuma ƙarfafa aniyarsu ta inganta tsarin dimokuraɗiyyar Nijeriya.
Tsoffin shugabannin biyu sun yabawa jam’iyyar bisa jajircewarta ga manufofin dimokuraɗiyya tare da kira ga ’yan Nijeriya da su haɗa kai domin tabbatar da dorewar dimokuraɗiyya a ƙasar.
“Dimokuraɗiyya na buƙatar haɗin kan dukkan ’yan Nijeriya. Jam’iyyun siyasa dole ne su ci gaba da taka rawar da ta dace domin tsarin dimokuraɗiyyarmu ya kasance mai ƙarfi kuma ya samar da kyakkyawan shugabanci ga al’umma.”
Janar Abdulsalami ya kuma yi addu’o’i domin zaman lafiya da farfaɗo da tattalin arziki a faɗin ƙasar, yana mai bayyana fatan cewa Nijeriya za ta shawo kan ƙalubalen da take fuskanta a halin yanzu.
“Wannan tattaunawa ta kasance mai matuƙar amfani. Mun samu shawarwari da za su ƙarfafa jam’iyyarmu tare da ba ’yan Nijeriya wata sahihiyar madadin jam’iyya yayin da muke fuskantar matsalolin rashin tsaro, cin hanci da rashawa, da talauci.”
Yarima Adebayo ya ce ingantaccen shugabanci na da matuƙar muhimmanci yayin da ƙasar ke shirin tunkarar babban zaɓe na gaba.
“Muna sake tsari a cikin jam’iyyar tun kafin zaɓen 2027. Jam’iyyun siyasa dole ne su fara gyara kansu kafin su iya samar da kyakkyawan shugabanci.”
Farfesa Gombe ya bayyana cewa ziyarar ta kuma kasance domin jajanta wa Janar Abdulsalami Abubakar game da rasuwar wasu ’yan uwansa, tare da neman addu’o’i da albarkarsa ga jam’iyyar.
“Da shugabanci mai gaskiya kuma mai mayar da hankali ga jama’a, Nijeriya na da damar cimma ci gaba mai ɗorewa.”
Jam’iyyar SDP ta ce wadannan ziyarce-ziyarcen na daga cikin tuntuba da dattawan ƙasa yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen zaɓukan da ke tafe.
0 Comments