Bangaren ilimi a jami’o’i masu zaman kansu a Nijeriya na samun sabon tagomashi a matakin duniya, inda sabbin bayanai ke nuna yadda suke samun ci gaba mai dorewa a fannin bincike, ayyukan malamai da gasa ta kasa da kasa.
A sakamakon bincike na shekarar 2026 na AD Scientific Index, wanda ke kimanta cibiyoyin ilimi ta hanyar amfani da bayanai na gaske, ya nuna cewa Nijeriya yanzu tana da jami’o’i 310, daga ciki 186 na gwamnati ne, 124 kuma na masu zaman kansu ne. Haka nan tsarin kimantawar ya lura da cibiyoyin bincike 24, kamfanoni biyar da asibitoci biyu, abin da ke nuna karuwar hadin gwiwa a tsakanin jami’o’i, masana’antu da cibiyoyin binciken kimiyya.
Duk da matsalolin tsare-tsare da suka dade tun kama daga karancin kudade zuwa gibin kayan aiki, jami’o’in kudi na Nijeriya na ci gaba da kara tasiri a fannin ilimi mai dogaro da bincike.
A saman jerin jami’o’in kudi na shekarar 2026 akwai Covenant University, wanda aka kafa a 2002 a Ota, Ogun. Jami’ar ta kasance ta farko a tsakanin jami’o’in kudi a Nijeriya kuma ta 221 a duniya, tana da masana 16 a tsarin kashi 10. Ayyukan jami’ar na nuna tasirinta mai karfi a fannin injiniya, fasaha da binciken amfani.
Sai dai, daya daga cikin muhimman ci gaban wannan shekara shi ne ci gaban da jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN) a Kano ta yi da saurin gaske. Ta kara samun tagomashin a tsakanin jami’o’i masu zaman kansu. An kafa jami’ar MAAUN ne a 2021, amma ta zama ta biyu a tsakanin jami’o’in kudi kuma ta 416 a duniya, tana da masana bakwai a cikin tsarin kashi 10. Wannan ci gaban da jami’ar MAAUN ta samu da saurin gaske na nuni da irin sabon karfinta ta hanyar bincike a tsakanin sabbin jami’o’in kudi na Nijeriya.
Sauran jami’o’in da suka yi fice sun hada da Afe Babalola University a Ado-Ekiti, Redeemer’s University a Ede, da Bowen University a Iwo—duk sun fadada shirye-shiryen sun a digiri na biyu da digiri na uku, karfafa kayan dakin gwaje-gwaje, da kuma neman hadin gwiwar bincike na kasa da kasa.
Cibiyoyin ilimi masu kwarewa kamar Landmark University a Omu-Aran da Bells University of Technology a Ota na nuna karuwar mayar da hankali a fannin noma, injiniya da kimiyyar amfani. Kazalika, African University of Science & Technology (AUST) a Abuja na ci gaba da kasancewa a sahun gaba a binciken kimiyya mai zurfi, a yayin da jami’o’i kamar Babcock University ke ci gaba da kasancewa mai muhimmanci a fannin bincike na kasa.
Gabaɗaya, bayanan sun tabbatar da cewa jami’o’in kudi suna kara zama jigo wajen bunkasar bincike a Nijeriya a lokacin da jami’o’in gwamnati da dama ke fuskantar karancin kudade da matsalolin yajin aiki dake addabar su. A yanzu haka, jami’o’in kudi na fafatawa don samun tallafin kasa da kasa, jawo hankalin malamai masu kwarewa a duniya, tare da shigar da hanyoyin bincike na kasa da kasa—abin da ke shimfida kyakkyawan makomar ilimi mai cike da gasa da kirkire-kirkire.

0 Comments