MAAUN Ta Bai wa Ɗalibai 43 Masu Daraja Ta Ɗaya Tallafin Karatu na Ƙasashen Waje



Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN) ta bai wa ɗalibai 43 da suka kammala karatu da daraja ta farko (First Class) tallafin karatu na ƙasashen waje a yayin bikin kammala karatu na farko da ta gudanar a ranar Asabar a Kano.

Wanda ya kafa jami’ar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ne ya sanar da bayar da tallafin a wajen taron, inda ya bayyana cewa tallafin zai ɗauki nauyin karatun digiri na biyu (Master’s) gaba ɗaya ga waɗanda za su ci gajiyar sa, a kowacce ƙasa da suka zaɓa.

Farfesa Gwarzo ya taya waɗanda suka kammala karatun murna tare da shawartar su da su zama jakadu nagari na jami’ar a duk inda suka samu kansu.

A nasa jawabin, Shugaban jami’ar MAAUN, Farfesa Mohammed Israr, ya ce jami’ar ta fara harkokin karatu ne a shekarar 2022 da shirye-shirye 15 a makarantu huɗu, kuma daga bisani ta faɗaɗa zuwa shirye-shirye 22 a makarantu takwas.

Ya bayyana cewa ɗalibai 492 ne suka kammala karatu daga shirye-shirye 12, inda suka haɗa da ɗalibai 43 suka fita da daraja ta farko, 220 da daraja ta biyu (Upper Credit), sai 229 da daraja ta biyu (Lower Credit). 

Shugaban majalisar jami’ar (Chancellor), Farfesa Mahamouda Salouhou, ya ƙarfafa gwiwar waɗanda suka kammala karatu da su riƙa kiyaye ƙimomi da manufofin jami’ar.

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda Shugaban Ma’aikatansa, Dr. Wali Sulaiman Sani, ya wakilta, ya tabbatar da ci gaba da goyon bayan gwamnatin jihar ga ɓangaren ilimi.

Fitacciyar dalibar da ta fi kowa ƙwazo wajen kammala karatu a jami'ar, Khadija Ibrahim Manzo daga Sashen Gudanar da lamuran al'umma (Human Resource Management), ta karɓi kyautar kuɗi har naira miliyan biyar (₦5,000,000) daga wanda ya kafa jami’ar.

Manyan jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, da masana ilimi daga sassa daban-daban na ƙasar nan ne suka halarci bikin kammala karatun.

Post a Comment

0 Comments