Jami'ar MAAUN Ta Karrama Marigayi Janar Abacha da Baré Maïnassara

Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN) ta bai wa tsohon Shugaban Ƙasa na Nijeriya, Marigayi Janar Sani Abacha, da kuma marigayi Shugaban Jamhuriyar Nijar, Ibrahim Baré Maïnassara, digirin girmamawa na 'Honorary Doctorate Degree' a fannin Jagoranci na bayan rasuwarsu.

An gabatar da wannan karramawar ne a yayin bikin kammala karatu karo na farko da jami’ar ta gudanar a harabar jami’arta ta Kano a ranar Asabar.

Alhaji Mohammad Abacha ne ya karɓi lambar yabo a madadin mahaifinsa marigayi Janar Sani Abacha, a yayin da Dr. AbdulRasheed Amadu ya karɓa a madadin marigayi Shugaban Ƙasar Nijar, Ibrahim Baré Maïnassara.

Da yake jawabi a wajen taron, wanda ya kafa jami’ar MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya ce an yi wannan karramawa ne domin girmama irin gudunmawar da shugabannin biyu suka bayar ga al'umma da ci gaban ƙasashensu.

A cewar Farfesa Gwarzo, jami’ar ta karrama marigayi Janar Sani Abacha ne bisa gagarumar gudummawar da ya bayar ta fuskancin shugabanci, fitaccen aikinsa na soja, da kuma gudunmawar da ya bayar wajen gina ƙasa da tafiyar da al’amuran mulki a Nijeriya.

Ya bayyana cewa a matsayinsa na Shugaban Ƙasa na soja, Janar Abacha ya nuna jagoranci mai ƙarfi da jajircewa, tare da mai da hankali kan daidaito da kwanciyar hankalin ƙasa.

Farfesa Gwarzo ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta ƙaddamar da manyan ayyukan more rayuwa da ci gaba, musamman ta hanyar shirin PTF. 

Ya bayyana cewa PTF na daga cikin manyan abubuwan tarihi da suka rage daga zamanin Abacha, inda ya aiwatar da ayyuka a faɗin Nijeriya kamar gina hanyoyi, kiwon lafiya, ilimi, samar da ruwan sha, da sufuri na al'umma, musamman a yankunan karkara.

Ibrahim Baré Maïnassara, tsohon shugaban soja, ya shugabanci Jamhuriyar Nijar har zuwa shekarar 1996, kafin a kashe shi a juyin mulki da ya faru a watan Afrilun 1999.

An bayyana cewa Baré ya taka rawar gani wajen haɗin gwiwar yankin da tattaunawar tsaro a Yammacin Afirka a wani lokaci mai cike da ƙalubale.

Da yake mayar da bayani a madadin iyalan Abacha, Alhaji Mohammad Sani Abacha ya nuna godiya ga jami’ar bisa wannan karramawa. Ya ce wannan girmamawa ba wai kawai ta amince da gudunmawar da marigayi Janar ya bayar ba ce, har ma tana tabbatar da dawwamar jajircewarsa ga ilimi, ci gaba, da kyawawan ɗabi’u da suka yi daidai da manufar jami’ar MAAUN, wadda aka sanya wa suna daga Hajia (Dr.) Maryam Sani Abacha, wadda ya bayyana a matsayin abar koyi wajen tausayi da ƙarfafa gwiwar al’umma.

Post a Comment

0 Comments