Daga Awwal Umar, Kontagora
Jami’an Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja, sashen STS, sun kama wani mutum mai suna Aminu Ahmed, mai shekaru 25, ɗan asalin Kontagora, bisa zargin sace yara da garkuwa da su tare da karɓar kuɗin fansa da ya haura Naira miliyan biyu.
An kama wanda ake zargin ne a ranar 27 ga Nuwamba, 2025, da misalin ƙarfe 7:00 na yamma, bayan samun sahihan bayanan sirri da jami’an tsaro suka tattara.
A yayin bincike, wanda ake zargin ya amsa cewa a cikin watan Janairu, 2025, ya sace wani yaro mai kimanin shekaru uku (3) a Unguwar Samaru, Kontagora, inda ya riƙe yaron tsawon kwanaki huɗu kafin ya tafi da shi birnin Legas.
Ya bayyana cewa a lokacin tafiyar, ya tuntubi mahaifin yaron tare da buƙatar kuɗin fansa har Naira miliyan goma (₦10,000,000), amma daga bisani ya karɓi Naira miliyan 1.4 (₦1.4m) ta hanyoyin POS daban-daban. Daga baya, ya dawo Kontagora inda ya bar yaron a kusa da wata tashar rediyo, yana ikirarin cewa yaron wanda aka tsinta ne, kafin ya tsere.
Haka kuma, bincike ya nuna cewa a watan Mayu, 2025, ya sake sace wani yaro mai shekaru huɗu (4) a Kontagora, ya tafi da shi Legas inda ya kwashe kwanaki uku. A wannan karon, ya nemi kuɗin fansa Naira miliyan goma, amma ya karɓi Naira dubu ɗari biyar (₦500,000). Daga bisani, ya dawo ya ajiye yaron a wani wuri a Karamar Hukumar Mashegu, inda ya sanar da iyayen yaron inda za su same shi.
A wani lamari na daban, a watan Nuwamba, 2025, ya sake sace wani yaro mai shekaru uku (3) a GRA, Kontagora, ya kai shi Ilorin, Jihar Kwara, inda ya riƙe shi tsawon kwanaki uku. Ya buƙaci kuɗin fansa Naira miliyan biyar (₦5,000,000), amma daga bisani ya karɓi Naira dubu ɗari uku da hamsin (₦350,000). Daga nan, ya bar yaron a Kaboji, dake Karamar Hukumar Mashegu.
Wanda ake zargin ya kuma bayyana cewa an yi masa asarar kuɗi sama da Naira miliyan 1.8 (₦1.8m) daga cikin kuɗaɗen da ya samu daga laifukan, sakamakon wani zuba jari na ma’adinai da ya shiga wanda ya ce an damfare shi.
A halin yanzu, Aminu Ahmed na hannun jami’an tsaro, yayin da Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja ke ci gaba da zurfafa bincike, tare da shirye-shiryen gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala bincike.

0 Comments