Jami'ar MAAUN Ta Ci Gaba da Zama Mafi Arha Cikin Jami’o’i Masu Zaman Kan Su A Nijeriya — Farfesa Gwarzo



Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN) ta ci gaba da kasancewa mafi arha a tsakanin jami’o’i masu zaman kansu a Nijeriya, duk da cewa an karrama ta a matsayin jami’a mai zaman kanta na biyu mafi kyau a ƙasar nan.

Wanda ya kafa jami’ar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ne ya bayyana hakan a yayin Bikin Cin Abincin Kammala Karatu karo na Farko da aka shirya ga daliban da suka kammala karatu a shekarar 2025 a harabar jami’ar ranar Alhamis.

Farfesa Gwarzo ya tabbatar wa iyaye da masu lura da ɗalibai cewa jami’ar tana jajircewa wajen samar da ilimi mai inganci da kwarewar karatu a farashi mai rahusa.

Haka kuma, ya shawarci iyaye da masu kula da ɗalibai da su riƙa tura duk korafinsu ta hanyar shugabancin jami’ar domin a magance su cikin lokaci, maimakon su ɗauki matsalolin zuwa kafafen sada zumunta.

Tunda fari, Shugaban jami’ar, Farfesa (Dr.) Mohammad Israr, ya yi maraba da iyaye, ɗalibai, da baki, inda ya bayyana taron a matsayin muhimmin tarihi ga MAAUN.

Mataimakin Shugaban Jami’a a bangaren gudanarwa, Dr. Habib Awais Abubakar, ya taya ɗaliban da suka kammala karatun murna sannan ya gode wa duk wadanda suka halarci bikin.

A sakon fatan alheri, Daraktan Cibiyar Turai ta jagoranci da ilimin dogaro da kai, Farfesa Mahamouda Salouhou, ya yaba wa Farfesa Gwarzo bisa kafa jami’ar. Ya bayyana cewa wannan kokari zai ƙarfafa mutane da dama su zuba jari a fannin ilimi, sannan ya taya iyaye murna bisa zaɓin MAAUN, wacce ke da haɗin gwiwa (MoUs) da manyan jami’o’i a Amurka.

Haka kuma, Farfesa Hakeem Ibukunle na Jami’ar Morgan State University, Baltimore, Maryland, USA, a sakon fatan alherinsa, ya taya ɗalibai da iyayensu murna kan cimma wannan mataki. Ya yaba wa wanda ya kafa jami’ar, Farfesa Gwarzo, bisa jajircewarsa wajen inganta ilimi a Nijeriya da ma duniya baki ɗaya.

A bangaren iyaye, Alhaji Sa’idu Bello da Abdulrahman Sulaiman Bawa Zaria sun gode wa wanda ya kafa jami’ar, Shugabanci, da ma’aikatan jami’ar bisa tarbiyyar da suka bai wa ɗalibai. Sannan sun taya ɗaliban da suka kammala karatu murna kan nasarar da suka samu.

Bikin cin abinci na kammala karatun ya haɗa ɗalibai, shugabanni, iyaye, da baki a cikin yanayi na jindadi.

Taron ya kasance cike da nishaɗi daga masu waka sanannu, Hamisu Breaker da Ahmerdy Mai Kallabi, tare da gabatar da wakar baka (spoken word).

Bakin taron ya more nau’ukan abinci na gargajiya da na ƙasashen waje, tare da abubuwan sha iri-iri da kayan marmari.

Post a Comment

0 Comments