Daga Awwal Umar Kontagora
Matasan Huffazil Qur’an da malaman addini na garin Gwada, cikin karamar hukumar Shiroro, sun gudanar da saukar Alkur’ani mai tsalki sau goma sha biyar tare da gabatar da addu’o’i na musamman domin kawo ƙarshen rashin tsaro da ke addabar ƙasar nan, musamman Jihar Neja da karamar hukumar Shiroro.
Mashawarci ga Gwamnan Neja kan harkokin makarantun tsangayu, kuma sakataren tsare-tsaren kungiyar ta jiha, Gwani Abdurrahman Sani, ya bayyana cewa gwamnati na farin ciki da irin waɗannan addu’o’in, musamman wajen kawo ƙarshen ayyukan ‘yan bindiga masu garkuwa da jama’a da tada tarzoma a ƙasa.
Da farko, uwar ƙungiya ce ke jagorantar irin wannan aiki a matakin jiha, yayin da kananan hukumomi ke ɗaukar nauyin gudanar da shi a lokuta daban-daban. Wannan aiki abin yabawa ne, kuma fatar Allah shi ne ya karɓi addu’o’in. Gwamnatin jiha ta yaba Gwani Ibrahim Yusuf da ya dauki nauyin shirya wannan kyakkyawan aiki a Gwada, ganin karamar hukumar Shiroro na cikin wuraren da ke fama da matsalar ‘yan bindiga.
Shugaban kungiyar ta jiha, Amb. Gwani Sheikh Hussain Abubakar Shakwata, ya ce Gwamna ya ɗauki ayyukan kungiyar da muhimmanci, musamman ganin cewa a kowanne lokaci yana bukatar Huffazil Qur’an su gabatar da addu’o’i idan matsaloli sun taso. Ya kuma nuna damuwa kan yadda ‘yan bindiga suka kutsa cikin wata makaranta a garin Papiri, karamar hukumar Agwara, inda suka kwashe dalibai sama da dari uku; bayan addu’o’in, an kubutar da dalibai dari, kuma ana fatar sauran zasu kubuta nan ba da jimawa ba.
Shugaban matasa na jiha, Gwani Muhammad Sirajo Shu’aibu, ya yaba wa matasan Gwada kan shirya saukar Alkur’ani da addu’o’in, inda ya bayyana wannan hanya a matsayin mai kyau. Ya kara da cewa wajibi ne iyaye su karantar da ’ya’yansu Alkur’ani kuma su koya masu sana’a, domin rage yawaitar matasa a ayyukan ta’addanci. Rashin fahimtar Alkur’ani da rashin riko da sana’a su ne manyan abubuwan da ke haddasa matsalar.
Sheikh Aliyu Tafida (Tafidan Kadiriya), daraktan harkokin da’awa na kungiyar, ya yi tsokaci kan sakacin al’umma wajen tallafawa malaman tsangayu, musamman wadanda ke koyar da Alkur’ani. Ya jaddada cewa iyaye da al’umma suna bai wa ilimin boko fifiko fiye da na addini, alhali ilimin addini yana kusantar da mutum ga Allah kuma yana haɗa ilimin boko da na addini domin wayewar kai ta gari.
Shehin malamin ya nuna muhimmancin ayyukan alheri, musamman kyauta da sadaka, inda ya ce Annabin Rahama (S.A.W) ya tabbatar mana cewa marowaci na nesa da Rahamar Allah, yana kusa da wuta, sannan yana kusa da aljanna idan ya yi alheri. Ya kuma jaddada cewa bai kamata a bar malaman addini cikin yanayin da zai sa su kauce wa tafarkin da ya dace ba.
Wannan taron shi ne na farko a garin Gwada, karamar hukumar Shiroro, kuma ya samu halartar manyan malamai da sarakunan gargajiya na gundumar Shiroro.

0 Comments