Ba Mu Yarda da Duk Wani Nau’in Rashin Gaskiya a Sana’armu ba – Inji S. Usman Estate

 

Daga Idris Umar, Zaria

Shugaban kamfanin S. Usman Estate Construction & Co. Ltd, Alhaji Sale Usman, ya bayyana cewa kamfaninsa ba ya yarda da duk wani nau’in rashin gaskiya a harkokin siyar da filaye da bayar da hayar gidaje da suke gudanarwa.

Alhaji Sale Usman, wanda ofishinsa ke Zangon Shanu a Ƙaramar Hukumar Sabon Gari ta Jihar Kaduna, ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai a ofishinsa a cikin makon nan.

Ya ce kafin kamfaninsu ya fara gudanar da sana’a, sun tabbatar da mallakar dukkan sahihan takardu da izini da doka ta tanada, domin kauce wa duk wata matsala tare da tabbatar da gaskiya da rikon amana a harkokinsu.

Shugaban kamfanin ya bayyana godiyarsa ga Allah Madaukakin Sarki bisa damar da ya samu duk da kasancewarsa matashi, inda ya ce hakan ya taimaka masa wajen samun rufin asiri da kuma amincewa daga shugabannin al’umma.

Ya kara da cewa sana’ar siyar da filaye da bayar da hayar gidaje sana’a ce halal, sahihiya kuma amintacciya, wadda ake gudanarwa bisa ka’ida, duk da cewa ana fuskantar wasu kalubale a wasu lokuta.

Alhaji Sale Usman ya ce, baya ga neman na kai, kamfaninsu na bayar da gudummawa wajen inganta tsaro a al’umma ta hanyar tantance mutanen da ke sayen filaye da gidaje a yankin.

Bisa haka, ya yi kira ga hukumomin yankin da su ba kamfaninsa goyon baya domin su samu damar gudanar da sana’arsu cikin tsari da kwanciyar hankali.

Har ila yau, ya bayyana cewa kamfaninsu na samar da ayyukan yi ga matasa da dama, inda ya ce akwai matasa da yawa da ke aiki a ofishinsa da kuma cikin ƙungiyar masu bayar da hayar gidaje da siyar da filaye a Ƙaramar Hukumar Sabon Gari, abin da ke nuna gudummawarsu wajen rage zaman banza.

Sai dai ya nuna damuwarsa kan yadda wasu jami’an tsaro, musamman ‘yan sanda a yankin Samaru, ke takura musu maimakon ba su haɗin kai, inda ya ce ya dace a rika yin aiki tare domin inganta tsaro da ci gaban yankin.

A ƙarshe, Alhaji Sale Usman ya yi kira ga matasa da su dage wajen rungumar sana’o’i, komai ƙanƙantarsu, domin dogaro da kai da kula da iyalansu.

Wasu daga cikin sarakuna da masu unguwanni a yankin sun kuma tabbatar da amincewarsu da irin gudummawar da Alhaji Sale Usman ke bayarwa, tare da shaida masa kyawawan halaye da mutunta jama’a.

Post a Comment

0 Comments