Ana Zargin Hukumar Zaɓe ta Jihar Neja da Riƙe Haƙƙoƙin Ma’aikatan Zaɓen da ya Gabata

 

Daga Awwal Umar Kontagora

Rahotannin da ke fitowa daga ƙungiyar Good Governance and Transparency of Nigeria, reshen Jihar Neja, sun nuna zargin cewa shugabancin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Neja (NSIEC) ya kasa yin bayani dalla-dalla kan yadda aka kashe kuɗaɗen da suka kai kimanin naira biliyan 1.5.

Ƙungiyar ta ce Shugaban NSIEC, Engr. Imam Mohammed, tare da Kwamishina na biyar mai kula da harkokin kuɗi da kaya, Hon. Kabiru Zama, ya dace su fito su bayyana gaskiyar yadda aka tafiyar da waɗannan kuɗaɗe.

Engr. Imam Mohammed shi ne Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Neja (NSIEC), kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC a jihar.

Bayan rantsar da mambobin hukumar, Gwamnan Jihar Neja, Umar Mohammed Bago, ya amince da biyan naira miliyan 100 a matsayin kuɗin fara aiki (take-off grant) domin bai wa hukumar damar gudanar da ayyukanta cikin yanayi mai kyau.

Haka kuma, bayan fitar da jadawalin zaɓen ƙananan hukumomi na shekarar 2025, rahotanni sun nuna cewa Gwamnan ya amince da ƙarin naira biliyan 1.3 domin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi na shekarar 2025.

Baya ga haka, hukumar NSIEC ta samu ƙarin kuɗi har naira miliyan 100 daga sayar da fom ɗin takarar zaɓen.

Sai dai duk da wadannan makuddan kuɗaɗe da aka amince da su, ana zargin cewa jami’an zaɓe ba a biya su haƙƙoƙinsu yadda ya kamata ba, lamarin da ya jefa ma’aikatan cikin damuwa.

Rahotanni sun nuna cewa ma’aikatan hukumar da dama sun fara nuna rashin jin daɗinsu, inda suka rubuta wasiku domin tunatar da hukumar kan haƙƙoƙinsu, tare da kai kukansu kafafen yaɗa labarai domin neman taimakon hukumomin jihar.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumar NSIEC ba ta fitar da wata sanarwa ta martani kan wadannan zarge-zarge ba.


Post a Comment

0 Comments