Za Mu Bai Wa ‘Yan Takarar APC Ƙuri’u Fiye da Na 2023 — Umar Erena

Daga Awwal Umar Kontagora

Kodinetan kula da harkokin jin daɗin matasa ga Gwamnan Jihar Neja, Dokta Umar Adamu Erena, ya bayyana cewa ofishinsa ya shiga haɗin gwiwa da ƙungiyoyin matasa domin tabbatar da cewa Gwamna Umaru Mohammed Bago da sauran ‘yan takarar jam’iyyar APC za su samu ƙuri’u fiye da waɗanda jam’iyyar ta samu a zaɓen shekarar 2023.

Dokta Erena ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a safiyar Lahadin da ta gabata a birnin Minna.
Ya ce duk da ƙalubalen tattalin arzikin da ƙasar ke fuskanta, gwamnatin Gwamna Umaru Bago ta kafa tarihi cikin kankanin lokaci, ba a Jihar Neja kaɗai ba har ma da ƙasa baki ɗaya. A cewarsa, hakan ya nuna nasarorin da gwamnati ke samu a fannoni daban-daban.

“Idan matasa suka ci gaba da mara wa wannan gwamnati baya, muna da tabbacin cewa Jihar Neja da Arewa gaba ɗaya za su yi alfahari da salon mulkin Gwamna Umaru Bago,” in ji Erena.

Ya ƙara da cewa gwamnan ya cika alƙawarin da ya ɗauka na bai wa mata dama a harkokin shugabanci. “Bayan zaɓen ƙananan hukumomi, a ƙananan hukumomi 25 na jihar, mata ne ke riƙe da muƙaman mataimakan shugabannin ƙananan hukumomi,” in ji shi.
Dokta Erena ya kuma nuna manyan ayyukan raya ƙasa da gwamnatin ke aiwatarwa, inda ya ce ko a Minna kaɗai, ayyukan raya ƙasa da ake gudanarwa a halin yanzu ba a taɓa ganin irinsu tun kafuwar jihar ba, balle a faɗa dukkan ƙananan hukumomi ana aiwatar da makamantansu.

Ya bayyana cewa tun kafin zuwan gwamnatin Umaru Bago, akwai ƙungiyoyin matasa da ke mara mata baya, kuma suna da tsare-tsare masu inganci. A cewarsa, ofishinsa ya haɗa waɗannan ƙungiyoyi wuri guda, ya tantance su, tare da yin aiki tare da su a zaɓen da ya gabata, kuma su ne za a sake haɗa hannu da su domin ci gaba da tallafa wa gwamnati a zaɓe mai zuwa.

Dangane da harkar katin zaɓe, Dokta Erena ya ja hankalin matasan jihar da su tabbatar sun mallaki katin zaɓe, yana mai cewa katin zaɓe ya fi makami muhimmanci a harkar siyasa. Ya jaddada cewa gwagwarmayar siyasa ita ce samun nasara ta hanyar zaɓe, ba tare da tashin hankali ko rashin mutunci ba.
A ƙarshe, ya yi kira ga matasa da su rungumi mutunta kai, zaman lafiya, haƙuri da jajircewa, yana mai cewa waɗannan su ne ginshiƙan ci gaba da samar da zaman lafiya mai ɗorewa.

Post a Comment

0 Comments