Daga Awwal Umar Kontagora
An jaddada cewa haɗin kan Musulmi shi ne ginshiƙin ƙarfinsu, kuma ya fi muhimmanci fiye da rarrabuwar kai, domin duk lokacin da aka rabu sai ya fi sauƙi a haddasa baraka a tsakaninsu. Wannan bayani ya fito ne daga Sayyadi Nasiru Almaliky, jikan marigayi Sheikh Muhammad Nasiru Kabara, bayan kammala jawabinsa kan iyalan Manzon Allah (SAW) a wajen Mauludin Kadiriya da aka gudanar a gidan Tafidan Kadiriya, Sheikh Aliyu Tafida, da ke bayan Dana a unguwar Maitumbi, Karamar Hukumar Chanchaga, Jihar Neja.
Almaliky ya bayyana cewa muhimmin abin da ya kamata Musulmi su rike shi ne Alƙur’ani mai girma tare da bin Sunnar Manzon Allah (SAW), inda ya ce wannan ne kadai zai kai al’umma ga rabauta a duniya da lahira. Ya kuma yi kira ga malamai da su guji fatawowi ko kalamai da za su janyo rarrabuwar kai, yana mai jaddada cewa Musulmi al’umma guda ce kamar yadda Allah Ya sanar a cikin Alƙur’ani.
A cewarsa, duk wani abu da zai janyo rarrabuwar kai ba daga Musulunci yake ba. Ya ce inda ake samun sabanin fahimta ya dace a zauna a warware shi, domin abubuwan da Musulmi suka haɗu a kansu sun fi waɗanda suka rarrabu a kai yawa. “Rarrabuwar kai ba ta kawo wa Musulunci komai illa rauni; idan kuka yi sabani kuka cutar da junanku, Allah zai gusar da kwarjininku,” in ji shi.
Shi ma Sheikh Hamza Muhammad Bello, Sarkin Malaman Bosso, ya yi jawabi kan bambancin akida, inda ya ce ma’aunin auna duk wani ra’ayi shi ne Alƙur’ani. Ya ƙara da cewa kalma guda ce ta haɗa Musulmi wato La ilaha illallahu Muhammadur Rasulullah. Ya yi nuni da cewa muddin wani ra’ayi bai sabawa Musulunci ba, ya kamata a rungumi juna tare da haɗa kai don ciyar da addini gaba.
Sheikh Hamza ya bayyana damuwa kan yadda ake cin mutuncin addinin Musulunci a yau da kuma raunana shi, duk da cewa Allah Ya nuna wa makiyan Musulunci cewa addinin nasa ne kuma ba zai gushe ba. Ya yi kira ga Musulmi da su koma kan koyarwar Alƙur’ani da Hadisi tare da riko da iyalan Manzon Allah (SAW) domin samun mafita ga matsalolin duniya da lahira.
A nasa bangaren, Sheikh Aliyu Tafida (Tafidan Kadiriya), Daraktan Da’awa na Huffazul Qur’an and Scholars Association of Nigeria, reshen Jihar Neja, ya bayyana cewa Mauludin bana ya zo da nasarori masu yawa. Ya ce an samu matasan malamai da suka gabatar da karatuttuka kan Manzon Allah (SAW), ciki har da Sheikh Nasiru, kaninsa Abul-Amanah, da kuma Sheikh Gwani Maliya, ɗan Sheikh Gwani Bello Beri. Ya yaba da irin gudunmawar da al’ummar Bayan Dana suka bayar, wanda ya sa Mauludin ya samu karɓuwa fiye da shekarun baya.
Sheikh Aliyu Tafida ya kuma nuna jin daɗinsa da yadda malamai suka yi karatu da fuska guda, dukkansu suna mai da hankali ne kan rayuwa da darussan Manzon Allah (SAW). Ya jaddada cewa idan aka ɗauki rayuwar Manzon Allah da iyalansa abin koyi, tabbas za a samu hanyar kubuta a duniya da lahira.
Taron Mauludin ya samu halartar shugaban Huffazul Qur’an and Scholars Association of Nigeria, Sheikh Gwani Hussaini Abubakar Shakwata, tare da shugabannin ƙungiyar Kurra’u ta Jihar Neja. A yayin taron, ƙungiyar ta kuma miƙa takardun shaidar fara aiki ga mambobinta daga shugaban jiha zuwa sauran mukarraban gudanarwa.
Haka kuma, gwannai sun kwashe dare suna karatun Alƙur’ani mai tsarki, inda zuwa sallar Asuba aka kammala saukar Alƙur’ani tare da gabatar da addu’o’i na musamman ga ƙasa kan matsalolin tsaro da kuncin rayuwa da al’umma ke fuskanta. Limamin Gwada, Sheikh Abubakar Sadiq, ne ya jagoranci addu’o’in.
0 Comments