Wakilin Daily Struggle a Jihar Neja Ya Zama Darakta Janar na Yaɗa Labarai na Huffazul Qur’an

Daga Wakilinmu

Wakilin jaridar Daily Struggle/Madogarar Labarai a Jihar Neja, Awwal Umar Kontagora, ya samu nadin Daraktan Janar na Yaɗa Labarai (DG Media) na ƙungiyar Huffazul Qur'an and Scholars Association of Nigeria, reshen Jihar Neja.

An mika masa takardar tabbatar da fara aiki (certificate of appointment) ne a yayin wani biki na musamman, inda shugaban ƙungiyar a Jihar Neja, Amb. Gwani Hussaini Abubakar Shakwata, ya bayyana cewa majalisar amintattu tare da sauran masu ruwa da tsaki a ƙungiyar ne suka yanke shawarar ba shi wannan muƙami.

A cewarsa, an yi nadin ne sakamakon rawar gani da Awwal Umar Kontagora ke takawa wajen yaɗa manufofi da ayyukan ƙungiyar ta kafafen watsa labarai, lamarin da ya taimaka matuƙa wajen wayar da kan al’umma da kuma fahimtar manufar tafiyar ƙungiyar.

“Mun ba ka wannan dama ne bisa cancanta. Muna fatan ba za ka yi ƙasa a gwiwa ba, sai dai ka yi amfani da wannan muƙami wajen ƙirƙiro sabbin dabaru da hanyoyin da saƙon ƙungiyar zai ci gaba da isa ga al’umma fiye da yadda yake a yanzu,” in ji Shakwata.

A nasa jawabin, Amb. Gwani Musa Adamu Hadeja, mai kula da yankin Arewa ta Tsakiya na Center for Qur’anic Reciters, ya bayyana cewa ba wa Malam Awwal Umar Kontagora wannan muƙami abu ne da aka yi da hangen nesa, la’akari da jajircewarsa a aikin jarida. Ya bayyana shi a matsayin mutum mai ƙwazo, himma da jajircewa wajen sauke nauyin da aka ɗora masa.

Baya ga wakilin jaridar, shugaban ƙungiyar a matakin jiha, Gwani Hussaini Abubakar Shakwata, tare da sauran mambobin shugabanci na jiha da shiyyar Neja ta Arewa, su ma sun karɓi takardun fara aiki a lokaci guda, kamar yadda kundin tsarin dokoki da ka’idojin ƙungiyar suka tanada.

Post a Comment

0 Comments