BOT ta miƙawa Shakwata muhimman takardun Huffazu

Daga Awwal Umar Kontagora

Majalisar amintattu ta kungiyar Huffazul Qur'an And Scholars Association of Nigeria, ta mikawa shugaban kungiyar ta jihar Neja, Gwani Hussaini Abubakar Shakwata muhimman takardun da ke dauke da tsare tsaren ayyukan kungiyar tare da dokokin kungiyar ta jihar Neja.

Mika takardun kama aikin ya biyo bayan amincewa da kamun ludayin shugaban jiha, Gwani Hussaini Shakwata na dan lokaci tun bayan rasuwar shugaban kungiyar, Gwani Abubakar Sadiq Maiturare.

Takaitaccen taron da ya samu halartar mataimakin shugaban kungiyar ta kasa mai kula da yankin arewa ta tsakiya, Amb. Gwani Musa Adamu ya gudanar ranar asabar a majalisin alarammomi da ke gidan sarkin Hausawan Minna.

Da yake bayani, shugaban kwamitin amintattun, Gwani Sani Isma'il, yace jinkirin mika wadannan kundin bayanan ya biyo bayan tsaikon da aka samu na ganin an shigar komai na daga cikin ayyukan da marigayi Maiturare ya gudanar karkashin jagorancin kungiyar.

Gwani Sani, yace ganin Sheikh Hussaini Shakwata, bai yi kasa a guiwa ba tun mika ragamar jagorancin kungiyar, yasa suka tabbatar sun bi ka'ida kamar yadda doka ta tsara na mika dukkanin kaddarorin kungiyar a hannunsa.

"An samu nasarori da dama, wanda shi ya janyo kungiyar ke ta kara samun tagomashi da karbuwa a gurin malaman tsangayu da gwamnati*.

Ina mai jawo hankalin shugaba Gwani Hussaini Abubakar Shakwata, da abokan aikinsa da su kara kaimi, wajen hadin kai, samar da maslaha a matsalolin da makarantun tsangayu ke ciki, da kuma ganin an cigaba da marawa manufofin gwamnati na inganta tsarin makarantun tsangayu a jihar Neja.

A na shi jawabin, wakilin shugaban Center for Qur'anic Receiters, kuma shugaban kungiyar mai kula da arewa ta tsakiya, Amb. Gwani Musa Adamu ya yabawa kwamitin amintattun bisa jagorancin, Gwani Sani Isma'il kan rike amana da kulawa tafiyar da kungiyar bisa manufar da aka kafa ta.

Haka kuma ya jawo hankalin shugaban na jiha, da ya cigaba da jajircewa kamar yadda ta samo kafin wannan lokacin, domin a dan kankanin lokaci ya samu nasarorin da ba za kirguwa.

An gudanar da addu'o'in zaman lafiya ga kasa da jihar Neja, da shugabancin kungiyar ta jiha. Gwani Adamu Maigidan Laka, shi ne aka nada a matsayin mataimakin shugaban kungiyar ta jiha.

Wasu daga cikin shugabanni a matakin kasa, da yankin arewa ta tsakiya da jihar Neja sun halarci shaidar karban takardun.

Post a Comment

0 Comments