Daga Ali Kakaki
Hajia (Dr) Maryam Sani Abacha ta karɓi digirin girmamawa na bayan rai da aka ba wa mijinta marigayi, tsohon Shugaban Kasa na Nijeriya, Janar Sani Abacha, daga Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN), inda ta bayyana wannan girmamawa a matsayin wacce ta dace a daidai wannan lokacin duba da irin aikin sa.
Janar Abacha ya mulki Nijeriya a matsayin Shugaban Kasa daga 1993 har zuwa rasuwarsa a 1998, lamarin da har yanzu ake nazari da muhawara akai game da salon shugabancinsa da manufofinsa.
Karɓar wannan digiri na girmamawa ya faru ne a gidanta dake Abuja, inda ta karɓi takardar bayar da digirin a madadin iyalin Abacha.
Ta yi godiya ga shugabannin jami’ar da kuma ‘yan Nijeriya gaba ɗaya, inda Hajia Abacha ta ce wannan girmamawa na nuna ƙoƙarin da marigayi janar ya yi wajen hidima ga ƙasa.
“Mun yi matuƙar farin ciki da alfahari cewa jami’ar ta girmama tsohon Shugaban Kasa, mahaifin wannan iyali, da digirin girmamawa na musamman. Alhamdulillah. Wannan girmamawa wacce ta cancanta ne. Ya yi aiki tukuru sosai,” in ji ta.
Ta bayyana cewa lokacin da aka zaba domin wannan girmamawa ya yi daidai da lokacin da al’umma ke ƙara tunawa da aikinsa a lokacin mulkinsa. “Mutane da yawa na tuna aikinsa musamman a waɗannan kwanaki. Lokaci ne mai kyau kuma abin alfahari ne cewa jami’ar ta girmama ayyukansa na baya, kamar yadda mutane ke girmama shi,” ta ƙara da cewa.
Hajia Abacha ta yi addu’o’i ga ruhin Janar Abacha tare da addu’ar Allah ya bunƙasa jami’ar.
Haka kuma, ta taya ɗaliban da suka kammala karatu a MAAUN murna, tare da ƙarfafa su da su kasance masu fata mai kyau duk da ƙalubalen tattalin arziki da ƙarancin ayyukan yi a ƙasar.
“Ina taya ɗaliban da suka kammala karatu murna, kuma ina yi musu fatan alheri a rayuwa. Ko da yake ayyukan yi sun yi karanci, ina addu’ar Allah ya basu aikin yi, kuma idan ya yiwu, za mu yi ƙoƙarin tallafa wa wasu daga cikinsu,” in ji ta.
Jami’ar ta sanar da cewa taron bikin bayar da digirin na bayan rai zai gudana ne a bikin kammala karatu da aka shirya yi a ranar 20 ga Disamba, 2025 a harabar MAAUN dake Kano.
Ana sa ran wannan biki zai zama ɗaya daga cikin manyan abubuwan da jami’ar ta tsara a jadawalinta, inda ake sa ran haɗuwar ɗalibai masu kammala karatun, jami’an jami’ar da baƙi da aka gayyata.

0 Comments