Kotu Ta Saki Gawarwakin Almajiran Shaikh Zakzaky Huɗu Da Sojoji Suka Kashe: Dubban Al’umma Sun Yi Musu Jana’iza a Zariya

An gudanar da jana’izar mabiya Harkar Musulunci guda huɗu a muhallin Darur Rahma da ke Dembo, Zariya a Jihar Kaduna, bayan kotu ta bayar da umurnin mika gawarwakinsu da aka ajiye tun bayan muzaharar goyon bayan Falasɗinu da aka yi a birnin Tarayya Abuja a ranar 28 ga Maris, 2025.

Jana’izar ta gudana ne a ranar Laraba, 24 ga Disamba, 2025, wanda ta yi daidai da 4 ga watan Rajab, 1447, tare da halartar dimbin al’umma, iyalai, abokan arziki da almajirai na Shaikh Ibraheem Zakzaky.

Wadanda aka yi wa jana’izar sun haɗa da: Kabiru Usman, Huzaifa Muhammad Sani, Jafar Abdullahi da Uzairu Zakariya.

Babbar kotu a Abuja ce a karkashin mai shari’a Gambo Garba, ta umarci rundunar ‘yan sanda da asibitoci da dama — ciki har da Asibitin Kasa na Abuja, Babban Asibitin Wuse, Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja da ke Gwagwalada da kuma cibiyoyin ajiye gawarwaki — da su mika gawarwaki guda takwas, inda hudu daga cikinsu aka riga aka yi musu jana’iza, saura hudu ake jiran mika su.

“Ba za mu daina gwagwarmaya ba” — Mu’assatus Shuhada

Shugabar Mu’assatus Shuhada, Maryam Sani Argungu, ta bayyana cewa waɗannan shahidai sun rasa ransu ne sanadiyyar harbin da sojoji suka yi yayin muzaharar Kudus.

Ta ce gidauniyyarsu na kula da iyalan waɗanda suka rasu, ciki har da matansu da ‘ya’yansu, tare da tabbatar musu da tallafi.

“Mun san wannan tafarki na gwagwarmayar tabbatar da adalci ba ya rasa jarabawa. Malam Zakzaky ya sanar da mu tun farko cewa akwai kisa, akwai dauri, akwai kamu. Duk da haka ba za mu fasa abin da muka fara ba,” in ji ta.

Ta kuma yi kira ga hukuma da ta saki ragowar gawarwakin hudu da ke sauran asibitoci.

Jin ta bakin iyalai

Sabira Ibrahim daga Suleja, ta bayyana cewa ta halarci jana’izar mijinta Uzairu Zakariya, inda ta ce: “Mun gode wa Allah bisa abin da ya same shi. Fatanmu Allah ya ba shi mafaka tare da sauran shahidai.”

Ɗansa, Bakir Uzairu, ya ce duk da jin zafin rashin mahaifi, suna alfahari da matsayin da ya samu na shahada: “Ba mu dana sanin bin wannan tafarki. Mun san tafarkin gwagwarmaya ne na gaskiya.”

Shima Muhammad Sani Suleiman, mahaifin Huzaifa, ya bayyana cewa: “Muna bakin cikin rabuwa da shi, amma ba mu bakin ciki da abin da Allah ya zaɓa masa ba. Muna addu’ar Allah ya karɓi shahadarsa.”

A nasa ɓangaren, Shamsiyya Usman Ali daga Kaduna ta tuna ɗan uwanta Kabiru Usman a matsayin mutum mai haƙuri: “Ina fatan Allah ya saka shi cikin rahama.”

Mabiya Harkar Musulunci sun ce za su ci gaba da fafutukar da suke yi domin tabbatar da adalci, tare da sake kiran gwamnati ta gaggauta mika ragowar gawarwakin da aka hana su na tsawon watanni.

Post a Comment

0 Comments