Farfesa Gwarzo Ya Bai Wa Alliance Française Kano Tallafin Naira Miliyan 10 Da Ginin Bene Mai Tsawo Biyu, Tare da Kayan Aiki Na Zamani


Wanda ya kafa gamayyar jami’o’in MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya bai wa Alliance Française Kano ginin bene mai hawa biyu da aka kammala da dukkan kayan aiki na zamani—ciki har da ajujuwan karatu na zamani, dakunan koyon harshe na zamani, dakunan multimedia, da kujeru da tebura na musamman da aka tsara don inganta koyarwa.

Fitaccen mai bunkasa harkokin ilimin ya ƙara tabbatar da irin jajircewarsa wajen bunƙasa ilimi da kuma musayar al’adu, ta hanyar ƙara bayar da tallafin Naira miliyan 10 domin gudanar da ayyukan yau da kullum da kuma tabbatar da dorewar cibiyar.

Ginin da jakadan Faransa a Nijeriya, Marc Fonbaustier, tare da Farfesa Gwarzo suka kaddamar da shi ga al’umma, ya ƙunshi allunan koyarwa na zamani, na’urar intanet mai ƙarfi, ɗakunan taro, kayan koyar wa da ke amfani da sauti da hoto, da kuma dakunan karatu na dijital.

Ginin da ke Ahmadiyya Junction a kan titin filin jirgin sama na Kano, yanzu ana ɗaukarsa a matsayin ɗaya daga cikin cibiyoyin koyar da harshen Faransanci da al’adu a zamance a Arewacin Nijeriya.

A cewar Farfesa Gwarzo, kafa irin wannan cibiya ta zamani zai taka rawar gani wajen farfaɗo da ilimin harsuna biyu a Kano, tare da bai wa ɗalibai damar samun ingantaccen horo na harshen Faransanci a matakin duniya.

A jawabinsa, Jakadan Faransa a Nijeriya, Marc Fonbaustier, ya yaba wa Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo bisa kyautar ginin da kuma samar da gagarumin kayayyakin da aka tanada a ciki.

Jakadan ya yi addu’ar Allah Ya kara wa Farfesa Gwarzo tsawon rai da lafiya, domin ya cigaba da bayar da irin wannan gudummawa ta jinƙai da kuma bunkasa ilimi wanda ya shahara da su.

Daraktan Alliance Française Kano, Ali Dabo, ya bayyana matukar godiyarsa ga Farfesa Gwarzo bisa ginin da kuma kayayyakin zamani da ya samar.

Ya ce a tsawon shekarun da cibiyar ta fara aiki a Kano, babu wani mutum da ya taɓa gyara wa ko sauya tsarin cibiyar, balle ɗaukaka ta zuwa wannan mataki na musamman kamar yadda Farfesa Gwarzo ya yi.

Ya ƙara da cewa, Farfesa Gwarzo ya kawo ƙarshen dogon lokacin da cibiyar ta shafe tana zaman haya fiye da shekara goma, ta hanyar samar mata da ofishi na dindindin kuma mai daraja.



 

Post a Comment

0 Comments