Jami'ar MAAUN Ta Yi Ta'aziyyar Rasuwar Mahaifiyar Tsohon Ministan Lantarki, Bashir DalhatuHukumar gudanarwa ta Jami'ar Maryam Abacha American University of Nigeria (MAAUN), ta mika sakon ta'aziyyarta ga tsohon ministan Lantarki, Alhaji Bashir Dalhatu da Wazirin Dutse bisa rasuwar mahaifiyarsu da kuma kishiyarta wanda suka rasu a rana guda ta ranar 9 ga watan Yunin 2021. 


Mahaifiyar tsohuwar ministan, Hajiya Fatima Dalhatu ta rasu tana da shekara 85, a yayin da kishiyarta Hajiya Rukayya Dalhatu ta rasu tana da shekara 95. 

Sanarwar ta'aziyyar na dauke ne da sa hannun shugaban rukunin Jami'ar wanda aka rabawa manema labarai a Kano a ranar Asabar. 


A cewar sanarwar, rasuwar iyayen guda biyu, Hajiya Fatima da Hajiya Rukayya babban rashi ne ba kawai ga iyalinsu amma ga dukkanin kasar domin mamatan sun haifi shugabanni da suka bada gudummawa wajen ci gaban kasar tare da tabbatar da Nijeriya ta kasance dunkulalliyar kasa. 

"Shugaban rukunin Jami'o'in Maryam Abacha American University ta Nijeriya, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo a madadin hukumar gudanarwa na mika sakon ta'aziyyarta ga dukkanin iyalai da kuma 'yan'uwan mamatan", inji sanarwar. 


A karshe Farfesa Abubakar Gwarzo ya yi addu'ar Allah ya jikan mamatan ya kuma sanya su a aljannar Firdausi. Tare da bai wa iyalai hakurin jure rashin da suka yi. 

Post a Comment

0 Comments