Sardaunan Gombe: Hasken Rana Leka Gidan Kowa: Jamil Gwamna, Jagoran Da Yake Da Burin Cigaba Da Gina Jihar Gombe

Daga Ibrahim Sani Shawai 

Daga cincirindon jama’a na grassroots, zuwa karramawar sarautun gargajiya, daga goyon bayan mata da matasa zuwa amincewar ‘yan kasuwa, tafiyar Sardaunan Gombe na samun karɓuwa a sassa daban-daban na jihar Gombe.

A siyasa, akwai lokacin da mutum yake neman karɓuwa a wurin jama’a, sannan akwai lokacin da jama’a da kansu suke nuna masa karɓuwa. Wannan shi ne abin da ya sa taken “Sardauna: Rana Leka Gidan Kowa" ya dace da yadda ake kallon tafiyar Dr. Jamil Isyaku Gwamna, Sardaunan Gombe, ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe a ƙarƙashin jam’iyyar APC.

Sunan Sardauna ya zama sananne a wurare da dama, amma abin da ya fi jan hankali shi ne yadda goyon bayansa ke bayyana ta hanyoyi daban-daban: tarbar da ake yi masa a lokacin ziyara, haɗin kan ƙungiyoyi, goyon bayan matasa da mata, da kuma karramawar da ya samu daga wasu masarautun gargajiya. Waɗannan abubuwa na ƙara fito da hoton ɗan siyasar daya Dade yana gina mu'amala da dangantaka da jama’a daban-daban a faɗin jihar.

A ranar 18 ga Oktoba, 2026, al’ummar unguwar Pantami da ke birnin Gombe sun fito kwansu da kwarkwatarsu domin tarbar Dr. Jamil Gwamna a lokacin ƙaddamar da ofishin kamfen na APC a yankin. An ruwaito cewa dubban jama’a ne suka halarci taron, ciki har da matasa da mata, lamarin da ya jawo hankalin masu bibiyar siyasar jihar.

Irin wannan tarba tana da muhimmanci a siyasa domin tana ba da damar ganin yadda ɗan takara yake hulɗa da jama’a, da irin sha’awar da suke nuna wa tafiyarsa. Ga magoya bayansa, tarbar Yan unguwar Pantami wata alama ce ta ƙarfafa gwiwa da kuma nuna cewa saƙonsa na samun damar isa ga mutane daban-daban.

Sai dai abin da ya fi muhimmanci shi ne ci gaba da gina wannan hulɗa ta hanyar sauraron jama’a, fahimtar buƙatunsu da gabatar da tsare-tsaren da za su inganta rayuwarsu.

Ɗaya daga cikin abubuwan da suka ƙara fito da sunan Dr. Gwamna a fagen zamantakewar al’umma shi ne karramawar da ya samu daga wasu masarautun gargajiya daga bangarori daban- daban a Jihar.

Ga al’ummar da ke da alaƙa ta kut-da-kut da masarautunsu, irin waɗannan karramawa suna da ma’ana ta musamman. Suna nuna yadda hulɗar mutum da al’umma za ta iya wuce siyasa ta shiga fannin al’ada, zamantakewa da gudummawar ci gaba.

Karɓuwa mai ɗorewa tana buƙatar haɗa jama’a daga sassa daban-daban. A wannan fanni, hulɗar da ke tsakanin iyalan Dr. Gwamna da ƙungiyoyin mata, matasa da sauran masu ruwa da tsaki ta kasance ɗaya daga cikin abubuwan da ake haskakawa a tafiyarsa.

A ranar 9 ga Satumba, 2026, sama da mata 6,000 daga ƙananan hukumomi 11 da yankunan ƙananan hukumomi 13 na jihar sun halarci taron Gombe Women’s Unity and Progress Summit, wanda Dr. Zainab Jamil Gwamna ta shirya. Taron ya mayar da hankali kan haɗin kan mata, jagoranci da bunƙasa gudummawar mata ga ci gaban al’umma.

Haka kuma, ɗaliban da suka ci gajiyar shirin tallafin karatu na Sardauna Scholars sun bayyana goyon bayansu ga takararsa, tare da alƙawarin taimakawa wajen wayar da kan jama’a.

Waɗannan hulɗa suna da muhimmanci domin matasa da mata ba masu kallo ba ne kawai a tafiyar ci gaban al’umma. Su ne daga cikin waɗanda za su fi amfana idan aka samar da ayyukan yi, damar samun ilimi, tallafin sana’o’i da yanayin tattalin arziki mai inganci.

A ranar 19 ga Oktoba, 2026, ƙungiyar Nigeria Amalgamated Traders and Artisans Development Association ta bayyana goyon bayanta ga takarar Dr. Gwamna tare da alƙawarin taimakawa wajen wayar da kan jama’a.

Goyon bayan irin wannan ƙungiya yana da muhimmanci saboda ‘yan kasuwa da masu sana’o’i suna da tasiri kai tsaye a tattalin arzikin yau da kullum. 

Abin da ya fi jan hankali a tafiyar Sardaunan Gombe shi ne yadda sunansa ke bayyana a tattaunawar siyasa ta hanyar tarurruka, goyon bayan ƙungiyoyi da karramawar gargajiya. Wannan ya sa magoya bayansa ke kallon Sardaunan Gombe ya zama hasken Rana Leka Gidan Kowa, taken da ke bayyana faɗin hulɗarsa da karɓuwar da suke ganin yana samu a sassa daban-daban na Gombe.

Amma babban abin da jama’a za su ci gaba da dubawa shi ne yadda wannan karɓuwa za ta haɗu da manufofi masu inganci: bunƙasa noma, inganta ilimi da lafiya, samar da ayyukan yi, tallafa wa matasa da mata, da kuma ƙarfafa tattalin arzikin jihar.

A ƙarshe, siyasa ba ta cika da tarba da yabo kaɗai ba. Ana auna ta ne da yadda take iya sauya rayuwar jama’a. Tarbar da ake yi wa Sardauna, goyon bayan da wasu ƙungiyoyi ke bayyanawa da karramawar da ya samu suna daga cikin abubuwan da suka ƙara sanya tafiyarsa a cikin tattaunawar siyasar Gombe.

Sardauna Daki-Daki — karɓuwa a cikin al’umma, hulɗa da jama’a, da burin gina Gombe mai ci gaba.

Post a Comment

0 Comments