Daga Zainab Ango, Zariya
Jam’iyyar (APC) ta sake samun wani muhimmin ci gaba na siyasa a Karamar Hukumar Sabon Gari ta Jihar Kaduna, biyo bayan nasarar gudanar da Babbar Taron Komowa Jam’iyya wanda ya tara manyan jami’an gwamnati, shugabannin jam’iyya, masu ruwa da tsaki, da magoya baya daga sassa daban-daban na jihar.
Taron, wanda Iyalan Marigayi Alhaji Sale Anur (Gabasawa) suka shirya, ya shaida karɓar gagarumin adadin ‘yan jam’iyyar (PDP) da suka koma APC a hukumance, lamarin da ya ƙara ƙarfafa tushen jam’iyyar a matakin ƙasa a Sabon Gari.
Shugaban Karamar Hukumar Sabon Gari, Honorabul Shiekh Jamilu Abubakar Albani Samaru Zaria, ne ya jagoranci karɓar masu sauya sheƙa tare da shugabannin jam’iyya. Ya bayyana wannan komowa jam’iyya a matsayin babbar alama ta amincewa da jagoranci da manufofin ci gaban gwamnatin Uba Sani a Jihar Kaduna ne baki ɗaya
An gudanar da taron ne bisa jagoranci da hangen nesa na Mai Girma, Sanata Uba Sani, Gwamnan Jihar Kaduna, inda masu jawabi da dama suka jaddada cewa manufofinsa na kula da jama’a da tsarin mulki na haɗin kai ne ke ƙara jawo karɓuwar APC a faɗin jihar Kaduna baki ɗaya.
Haka kuma, Honorabul Muhammad Garba Datti Babawo, Mataimakin Shugaban APC na Yankin Arewa maso Yamma, ya halarci taron, inda ya yabawa shugabancin jam’iyya a Jihar Kaduna da kuma Sabon Gari musamman. Ya bayyana cewa wannan gagarumar komowa jam’iyya tana nuna sabon amincewa da APC ƙarƙashin jagorancin Gwamna Uba Sani shugaban yayi wa jama'ar ƙaramar hukumar Sabon Gari albishir na kwato bubban filin wasa na Sabon Gari da tsohon shugaban karamar hukumar Sabon Gari ya sayar.
Haka zalika ya kara yin tofin Altsine ga masu yin masu badakala a fadin karamar hukumar hukumar tasu.
Daga cikin manyan baƙin da suka halarcci taron akwai Rt. Honorable Aminu Abdullahi Shagali Kwamishinan Gidaje da Raya Birane na Jihar Kaduna; Honorabul Nasir Idris, ɗan Majalisar Dokokin Jihar Kaduna mai wakiltar Mazabar Sabon Gari; da Hon. Malam Sani Basawa, ɗan Majalisa mai wakiltar Mazabar Basawa. Sauran sun haɗa da Mataimakin Shugaban Karamar Hukuma Hon. Abdulkareem Kamilu da Honorabul Umar Uba Maichitta da Honorabul Abubakar Umar Yariman Bomo, tare da manyan jiga-jigan APC, shugabannin jam’iyya, shugabannin mazabu da magoya baya.
Masu jawabi a madadin Iyalan Gabasawa kamar Malam Muhammad Ibrahim da sauran yan'uwasa sun jaddada muhimmancin haɗin kai, daidaito a jam’iyya, da kuma ƙarfafa wayar da kan jama’a a matakin ƙasa domin dorewar karɓuwar APC. Sun kuma tabbatar da cikakken goyon bayansu ga hangen nesa na ci gaban Gwamna Uba Sani da kuma ƙarfafa tsarin APC a dukkan matakai.
Dr Ibrahim Hamidu ne ya rufe taron da addu'a.
0 Comments