Kungiyar Huffazul Qur’an Ta Gudanar da Addu’o’i na Musamman Ga Sabbin Shugabanni a Jihar Neja

 

Daga Awwal Umar, Kontagora

Kungiyar Huffazul Qur’an and Scholars Association, reshen Jihar Neja, ta gudanar da addu’o’i na musamman domin neman taimakon Allah ga sabbin shugabannin kananan hukumomi da kwamishinoni da gwamnatin Jihar Neja ta rantsar kwanan nan.

An gudanar da addu’o’in ne a Masallacin Juma’a na Shakwata, mahaifar Shugaban Karamar Hukumar Chanchaga, Hon. Mustapha Jibrin Alheri.

Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Kungiyar na Jiha, Gwani Sheikh Hussaini Abubakar Shakwata, wanda kuma shi ne Babban Limamin Juma’a na Shakwata, ya bayyana cewa an shirya taron ne domin saukar Alƙur’ani Mai Girma guda goma sha ɗaya (11) da kuma gudanar da addu’o’i na musamman, sakamakon ƙalubalen tsaro da jihar ke fuskanta.

Ya ce manufar taron ita ce neman mafita daga Allah (SWT), tare da roƙon Allah Ya ba wa sabbin shugabannin ikon sauke nauyin da ke kansu, yana mai jaddada cewa duk wata matsala za ta samu mafita idan aka mayar da lamari ga Allah.

Sheikh Hussaini ya ƙara da cewa irin waɗannan addu’o’i ana gudanar da su akai-akai, musamman a Babban Masallacin Juma’a na Minna, amma an zaɓi garin Shakwata a wannan karo ne saboda ɗaya daga cikin shugabannin da aka rantsar ɗan asalin garin ne, kuma yana daga cikin waɗanda suka assasa masallacin da aka gudanar da taron.

A nasa jawabin, Amb. Sheikh Musa Adamu, Limamin gidan Janar Ibrahim Badamasi Babangida, kuma Mataimakin Shugaban Kungiyar na Ƙasa mai kula da Arewa ta Tsakiya, ya bayyana cewa wannan saukar ita ce rufewa, bayan da aka gudanar da saukar Alƙur’ani sama da guda dubu ɗaya da ɗari (1,100) a makarantun tsangaya daban-daban a faɗin jihar.

Ya ce da saukar guda goma sha ɗaya da aka kammala a Shakwata, jimillar saukar da aka gudanar ta kai guda dubu ɗaya da ɗari da goma sha ɗaya (1,111).

Sheikh Musa ya jaddada cewa manufar addu’o’in ita ce Allah Ya riƙe hannayen shugabannin, Ya ba su ikon aiwatar da manufofi da za su haifar da ci gaba mai ɗorewa a Jihar Neja, wadda ya bayyana a matsayin jiha mai faɗi da kuma cike da ƙalubale.

Ya kuma yi addu’a ga Gwamnan Jihar Neja, da Shugaban Ƙasa, da sauran shugabanni, da Allah Ya ba su ƙwarin gwiwa da hikima wajen jagorantar al’umma, domin zaman lafiya, cigaba da bunƙasar ƙasa.

A nasa bangaren, Dan Azumi Muhammad, Wakilin Hausawan Shakwata kuma Wakilin Hakimin Shakwata, ya bayyana godiya ga Allah da Ya bai wa ɗan garin su, Hon. Mustapha Alheri, damar zama Shugaban Karamar Hukumar Chanchaga.

Ya kuma yaba wa al’ummar Chanchaga bisa goyon bayan da suka ba shi, tare da jaddada buƙatar haɗin kai da zaman lafiya a Shakwata, inda ya bayyana cewa garin ya ƙunshi kabilu daban-daban kamar Hausawa, Gbagyi, Nupawa, Kambari da Dakarkari, kuma suna zaune cikin kwanciyar hankali ba tare da nuna wariya ba.

Wakilin ya kuma jawo hankalin Hon. Mustapha Alheri, wanda ya taɓa rike mukamin Kwamishinan Lafiya, da ya ci gaba da amfani da ƙwarewarsa wajen kawo cigaba a Chanchaga, tare da jajircewa wajen daƙile rigingimu da ayyukan daba a tsakanin matasa.

An kammala taron cikin kwanciyar hankali, tare da fatan addu’o’in da aka yi za su kasance alheri ga shugabanni da al’ummar Jihar Neja baki ɗaya.

Post a Comment

0 Comments