Daga Awwal Umar Kontagora
Ƙungiyar Nigeria Union of Mine Workers (NUMW) ta sha alwashin ba da cikakken goyon baya ga Gwamnatin Jihar Neja domin habbaka hanyoyin samun kuɗaɗen shiga a ɓangaren ma’adanan ƙasa.
Shugaban ƙungiyar a Jihar Neja, Comrade Musa Adamu Nasko, ne ya bayyana hakan yayin da ya jagoranci shugabannin ƙungiyar na jiha da na ƙananan hukumomi zuwa ziyarar taya murna da fatan alheri ga sabon Kwamishinan Ma’aikatar Ma’adanan Ƙasa ta jiha, Hon. Mohammed Kasim Danjuma.
A cewarsa, ma’aikatar ma’adanan ƙasa ita ce uwar dukkan masu cin abinci a wannan fanni, don haka ya zama wajibi ƙungiyar ta ba da cikakken goyon baya domin ci gaban ma’aikatar da Jihar Neja baki ɗaya.
“Mun gamsu da salon mulkin mai girma Gwamnan Jihar Neja, Umar Mohammed Bago, na gina sabuwar Jihar Neja. Muna kuma da kyakkyawan fata cewa zuwan wannan sabon kwamishina zai kawo sauye-sauye masu amfani da za su bunƙasa hanyoyin samun kuɗaɗen shiga ga gwamnatin jiha. Mu a shirye muke mu yi aiki kafaɗa da kafaɗa da ma’aikatar domin cimma wannan buri na ci gaba,” in ji Nasko.
A nasa jawabin, sabon kwamishinan ma’aikatar, Hon. Mohammed Kasim Danjuma, ya nuna farin cikinsa da wannan haɗin gwiwa da goyon bayan da ƙungiyar NUMW ke bai wa gwamnati, inda ya tabbatar da cewa ma’aikatar za ta yi aiki tare da ƙungiyar domin cimma manufofin da aka sanya a gaba.
Kwamishinan ya bayyana cewa akwai wasu kamfanoni da gwamnatin jiha ta bai wa alhakin tattara haraji, amma bayan zuwansa ya gano cewa wasu daga cikinsu ba sa miƙa ainihin kuɗaɗen shigar da ake samu. Saboda haka, ma’aikatar ta dakatar da su na ɗan lokaci domin gudanar da bincike da kuma tsara sabbin matakai.
“Ba mun kore su ba, mun dakatar da su ne kawai har sai mun kammala bincike da tsare-tsaren da suka dace. Duk kamfanin da aka kama da laifi dole ne a hukunta shi. Gaskiya da rikon amana ne kaɗai za su ba da damar ci gaba da wannan aiki,” in ji shi.
Ya kuma gargaɗi kamfanonin da abin ya shafa da su guji karya doka, yana mai cewa duk wanda aka kama bayan dakatarwar nan lallai zai fuskanci fushin gwamnati.
A nasa jawabin, Comrade Abubakar Idris, Shugaban Ƙungiyar Kwadago a Ƙaramar Hukumar Borgu kuma Shugaban NUMW na ƙaramar hukumar, ya yaba da manufofi da ƙudurorin sabon kwamishinan.
Ya ce mambobin ƙungiyar a Borgu a shirye suke su mara wa dukkan tsare-tsaren gwamnatin jiha baya, muddin ba su saɓa wa dokokin ƙasa kan harkokin hakar ma’adanan ƙasa ba. Ya ƙara da cewa ƙungiyar ta jiha na da ƙwarewa wajen kare haƙƙi da mutuncin mambobinta, don haka za su ci gaba da ba da goyon baya ga shugabanni a matakin ƙananan hukumomi domin ci gaban harkar ma’adanan ƙasa a Jihar Neja.
Ziyarar ta samu halartar shugabannin ƙungiyar NUMW na jiha da na ƙananan hukumomi, inda aka tattauna muhimman batutuwa da suka shafi tsaro da hanyoyin inganta tattara kuɗaɗen shiga ga gwamnatin jiha.

0 Comments