Daga Bello Hamza, Abuja
Gwamnatin tarayyar Nijeriya, ta sha alwashin tabbatar da inganta tsarin koyar da karatun Allo da yadda ake gudanar da ilimin tsangayu a fadin kasar.
Ministan Ilimi na Nijeriya, Dakta Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan biyo bayan taron kaddamar da tsarin inganta koyar da Karatun Allo da ilimin Tsangayu na Bai-daya, wanda ya gudana a ranar Litinin din da ta gabata, a babban birnin tarayya Abuja.
Da ya ke yi wa manema labarai karin haske dangane da wannan gagarumin sauyi da ma’aikatar ilimin ke kokarin aiwatarwa, mai taimakawa Ministan ilimin kan ilimin Almajirai da Tsangayu da da Makarantun Allo, Dakta Balarabe Shehu Kakale, ya ce nan bada jimawa ba Makarantun Allo za su dinga gogayya da takwarorinsu na Boko da ke faÉ—in Kasar nan.
Kakale, wanda shi ne Barden Tsangayu da Makarantun Allo na Kasar Hausa, ya kara da cewa manufar samar da tsarin shi ne don ingata rayuwar Almajiran da ke lungu da saƙo na Nijeriya.
A cewar Dakta Kakale, “Kafin a kai ga wannan matsaya, sai da muka karade daukacin shiyyoyin siyasa shida na Nijeriya inda muka tattauna da masu ruwa da tsaki kamar Malamai da sarakuna harma da Kungiyar kiristoci ta Nijeriya (CAN), wanda kuma akwai bukatar ganin gwamnatocin jihohi sun kara zage damtse wajen kaiwa ga cikakkiyar nasara”.
Daga bisani ya yaba wa Ministan ilimin kasar Dakta Tunji Alausa, da Ministar Kasa a ma’aikatar ilimi, Dakta Suwaiba Ahmed, Shugaban hukumar Kula da ilimin Almajirai da Yaran da basa zuwa makaranta ta Nijeriya, Dakta Mohammed Sani Idris, harma jagororin addinai da sarakuna, bisa matakan da suke dauka na inganta ilimin Almajirai dama rayuwar Yaran da basa zuwa makaranta ta hanyar koyar da su sana’oin hannu wanda zai basu damar dogaro da kan su, a karkashin Shirin.

0 Comments